Sunday, 1 April 2012

Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare


Jam’iyyar PDP, wacce ake cewa  ta fi ko wacce girma da kasaita a Nahiyar Africa, ta yi babban taronta a karo na tara, inda aka ce ta nannada sababbin shugabanninta na kasa baki daya da za su ja ragamarta nan da wasu shekaru hudu masu zuwa. Amma sai dai abin mamaki game da wannan taron shine yadda ‘ya’yan jam’iyyar ba su nuna wani zumudi ko wata murna game da taron ba, kuma haka nan aka watse wasu na cewa tir; wasu kuma na cewa madalla. A takaice dai ana iya cewa yabon da aka yi wa jam’iyyar da ‘ya’yanta wajen shirya wannan taron bai kai yawan fallasar da aka yi ta yi ba, musamman saboda rashin armashin tsarin gudanar da taron da kuma kurar da hakan ta tayar.
Akan ce zai yi wuya a gasa kaza sannan a yar, ba za a ci ba. Irin abin da ya faru kenan bayan kammala nade-naden da suka biyo zazzare idanun da aka yi wa ‘yan takaran mukamai da yawa don su janye, su bar ‘ya’yan mowan da ake kira shafaffu da mai su tsaya takarar da za a ce sun janye ba tare da wata hamaiya ba. Bamanga Tukur, wanda aka yi ta kai ruwa rana don yin rufa-rufa da kumbiya-kumbiya wajen tsayar da shi takarar shugabancin jam’iyyar, aka bar shi, shi kadai don ya yi cara ba tare da wani ya kalubalance shi ba, shi ne kuma ya kalubalanci shugabannin jam’iyyar a jawabin amincewa da gatar da aka yi masa na hayewa karagar jam’iyyar da ba irinta a Najeriya, wanda a ciki ya yi jirwaye mai kama da wanka.
Duk da cewa ya nuna godiyarsa ga iyayen gidansa, wadanda suka dafa masa, amma ya nuna cewa jam’iyyar ta PDP ba sahihiya ba ce, ana tafka ta’asa da aikata kaba’irai wajen gudanar da harkokinta, kuma wajibi ne a yi gyararrakin da za su magance wadannan matsalolin da suka sa talakawa na guje mata kamar sabuwar kuturwa. Wadannan matsaloli kuwa sun hada da danniya da murdiya wajen bin tafarkin dimokuradiyya a harkokin sarrafa al’amuran da suka jibanci jam’iyyar, da kuma nuna wariya da bambanci wajen rarraba mukamai, da kuma rashin adalcin dake sanyawa ana yi da wasu, aka kuma mayar da wasu saniyar ware, ba a yi da su.
Wadannan muhimman batutuwa ne da bai kamata a ji sun fito daga bakin Bamanga ba, domin kuwa an ce idan maye na da hankali bai fitar da maitarsa a fili. Idan da Bamanga ya yi la’akari da yadda aka danka masa ragamar jam’iyyarsa, da bai furta haka ba, domin kuwa dukkan illolin da ya rattaba, wadanda yake kukan cewa su ne ke wahalar da jam’iyyarsu, da su ne aka yi amfani don daure masa gindi ya ci gaba da karfafa su a cikin jam’iyyar, domin kuwa ta kansu ake so ya bi don biyan bukatun wadanda suka cicciba shi hawa wannan mukamin.
Ba ma sai an dauki dogon lokaci wajen tonon silili game da yadda shuwagabannin jam’iyyar PDP suka dage lallai sai Bamanga ba, alhali kuwa ko a shiyyarsu ma sai da ‘ya’yan jam’iyyar suka karya masa tsinken tsire a ido, suka nuna masa iyakarsa a kwarya-kwaryar zaben fitar da dan takarar shugabancin jam’iyyar da aka yarjewa shiyyarsu ta fitar. Amma da yake babu gaskiya, ko da’a a cikin al’amarin siyasar kasar nan, sai gashi nan an biyo mutumin da aka kwance wa zani a kasuwa zuwa gida don a sake daura masa. Abin da haka nan ya nuna Bamanga ne kawai zai iya tankwara dokoki da ka’idojin jam’iyyar wajen share fagen sake tsayar da shugaba Jonathan takarar shugabancin kasa a 2015.
 Wannan ba wani sabon abu bane game da Bamanga, abu ne da ya saba, aka san zai iya, domin an sha yin amfani da shi wajen aiwatar da abubuwan dake cutar da jama’arsa. Ai ‘yan Arewa na sane da yadda ya haramta musu samun damar komo da mulki shiyyarsu a zaben 2011, lokacin da ya zama dan Arewa na farko da ya zake wajen goyon bayan dorewar Shugaba Jonathan, don bijire wa tsarin karba-karba na jam’iyyarsu. Ashe idan a yanzu an rama wa kura aniyarta da nadin da aka yi masa ba don komai ne ba, sai don ya ci gaba da aikin da ya fi kwarewa ne a kai, watau wawushe kafafun ‘yan siyasar Arewa, da kuma dakile burinsu na shugabancin kasar don su huce takaici, su kuma farfado da martabarsu a fagen siyasar Najeriya.
Idan kuma aka dubi take-taken jam’iyyar PDP a ‘yan shekarun da suka shude, sai a fahimci cewa ta zame tamkar makiyar Arewa da jama’arta, kuma manyan Arewa da ke cikinta sun kasance karnukan farautar ‘yan kudun da ke jan ragamarta, wadanda kuma ke kyamar dabi’u da al’adunsu da ma addininmu.  A halin yanzu dai babu wanda zai iya cewa ga makomar ‘yan Arewa a cikin jam’iyyar PDP, wacce ta gwanance wajen  yin kutun-kutun din wargaza duk wata jam’iyyar da talakawan Arewa suka runguma don tserar da su daga masifun da shugabannin cikinta ke haddasawa. Talakawan kasarnan a ko dayaushe fata suke yi Allah ya raba su da tsari ko mulki irin na jam’iyyara PDP wacce ba mai amfana da ita, daga manyan cikinta sai matansu, da farekaninsu da kawalansu da kuma karnukansu. Tuni talakawa suka dawo daga rakiyar shugabannin PDP, amma su a kullum gani suke har yanzu jama’a na tare da su, ba su kuma gane cutar da take yi musu..
Dangane da haka ana iya cewa babban taron jam’iyyar PDP da aka kamala a makon jiya ya kara fadakar da jama’ar Arewa cewa jam’iyyar PDP ba ta son mulki ya sake hauro wa Arewa, kuma babu abin da zai hana ta yi wa shugaba Jonathan aiki don ya sake darewa mulki a karo na biyu da kuma samun nasara wajen gyararrakin da ake son yi wa kundin tsarin mulki na 1999, don a kara tsawon wa’adin gwamnoni da shugaban kasa bisa mulki.
To ko wacce fuska aka kalli wannan al’amari sai a fahimci cewa, yana tattare matsalolin da za su iya tayar da zaune tsaye a kasar nan, musamman ma ganin yadda Shugaba Jonathan ke sha’awar lashe aman da ya yi na cewa, ba zai yi takara a 2015 ba, da kuma yadda ‘yan kabilar Ibo suka ja daga, suka ce idan ba za su karbi mulki ba a wannan karon to kasar ta bar zama lafiya kenan.

To gashi nan tun yanzu an ja daga kuma mai yawan rai zai yi kallon yadda za ta wanye tsakanin ‘yan shiyyar kudu maso kudu da za su nace lallai sai Jonathan ko wani nasu, da kuma Inyamurai da suka riga suka ci da zuci saboda zafin kawazucin mulki. Haka nan kuma za mu ga yadda batun addini zaiyi tasiri a 2015, domin kuwa da shi ne jam’iyyar PDP ta raba kan ‘yan Arewa har aka kaita aka baro. To idan a 2015 tsirarun shiyyar Arewa ta tsakiya, da ake kira middle belt, suka nemi tsayar da dan takaran shugabancin kasa bisa akidar addini, shin mutanen gabashin kasar da ke bin addini daya da su za su rama wa kura aniyarta kuwa daidai da yadda suka yi wa Jonathan a 2011?  Oho! Ai ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

SAKIYAR DA BA RUWA

“Najeriya ce Ƙasar da muke da ita, ba mu kuma da wacce ta fi ta. Wajibi ne mu kasance a cikin ta, mu kuma haɗa kai wajen kyautata makomar...