Siyasar zamanin yanzu, ko kuma in ce shiga takara ta zama kamar budurwa. Idan da yarinya za ta sangame a gari ta rasa manemi, har ta zo da kanta ta durkusa tana rokonka fuskar ta cike da hawaye sharkaf, cewa don Allah don Annabi ka rufa mata asiri ka aure ta, wata ma idan ba a gari guda kuke ba har ta yayimo kwamutsanta ta dawo domin kai, amma da zarar ka amince da kyar, to shikenan daga wannan lokaci da kace ka amince, kaine kuma ke neman ta, ba ita ce ke neman ka ba. Wato daga nan kai ne za ka rika zuwa wurinta zance, ka rika yi mata toshi, da kayan Sallah, idan yar makaranta ce, da sayayyar makaranta, kai ne kuma har ila yau za ka rika buga mata waya akai-akai, har ka kai ga yin kayan aure da bayar da sadaki. Tunda har ka shiga, to kai ne maneminta ba ita ce manemiyar ka ba. Duk wata wahala da ake yi wa ‘ya mace sai kayi iya bakin kokarin ka domin ka ga ka yi mata. Amma duk da haka ta rika jin cewa kai ne ka ke morewa ba ita ba, kuma ta rika ganin cewa ko a yanzu aka kawo ta gidan ka, ma kai aka taimaka wa, ba ita da tun da fari ka amince da kyar cewa za ka rufa mata asiri ka aure ta ba. Kai karshe ma ana kan haka, idan ka sake ta ci karo da wani wanda ya dan fi ka abin duniya to sai dai ka ji a salansa.
To haka ma siyasa take. Ban ce a da can ba, amma dai a halin yanzu haka take. Idan duk ‘yan garinku za su rika yiwo tawaga-tawaga, mota-mota suna zuwa wurinka, suna rokonka ka shiga siyasa ka yi takara, domin sun lura kana da kishi, kuma kai me kamanta gaskiya ne, to kyawunta kada ka kuskura ka amsa. Muddin dai ka kuskura ka amince, to shikenan ka zama kaine mai neman mukami. Daga nan sai a rika kiran ka ‘’mai neman mukami kaza a cikin jam’iyya kaza’’. Kai da aka neme ka, yanzu kuma reshe ya juye da mujiya, ana cewa kaine ka ke nema. Haka za a zuba maka ido, duk inda kudi suke sai ka yi ta fadi-tashin neman su kana batar da su ta hanyar su wadannan da suka yi ta rokonka ka zo ka shiga siyasa don ka ceto su. Tamkar dai yadda ita yarinyar nan da ta rokeka ka shiga neman ta, ita ce kuma za ta rika more kashe kudin da kake mata tun kafin ta shigo gidan ka.
To kaine mutane suka farauto ka, ka zo ka yi takara don ka yi musu aiki, domin sun lura kai mai kishi ne da tausayin jama’a, amma kuma sai ka nemo kudi duk inda suka shiga kana raba musu kafin su yi maka aikin da za a zabe ka. Duk da haka kuma, idan Allah yasa ka ci zabe a yi tsammanin ba za ka fara neman mai da kudin da ka kashe na lokacin kyamfe ba. Tabdi jan! ai idan ba wani mala’ika Allah ya saukar daga sama ba, babu wani mahalukin da ba haka zai yi ba. Haka ma idan dan takara yana da mutum daya, ko kuma (god father) a turance, wanda ya dauke masa duk nauyin wahalhalunsa na yakin neman zabe, to shima mutum dayannan fa yana so a ce bayan an gama kuma an ci nasara, to a maida masa abin da ya kashe duka gami da riba mai tsoka a kayi. Kai idan ma karo-karo, ko kuma taimako ‘yan uwa da abokan arziki suka yi ta bai wa dan takarannan, to za su so bayan ya hau mulki, ya maida musu abin da suka kashe masa da kuma nasu ribar.
Ire-iren wadannan munanan tsare-tsare da aka bijiro dasu, suke zama takin habbaka masifun da al’ummomi suka kasa yin ban-kwana da su a wannan kasar, musamman ma mu talakawa. Matsaloli kamar su rashin ingantattun shugabanni masu kaifin hankali da hangen nesa, da cin hanci da rashawa, da tsabar ha’inci da sace-sacen dukiyar talakawa. Duk wadannan sun samo asali ne a sakamakon son zuciyar shugabanni, da kuma son kan talakawan da ba sa iya tabuka komai don hanawa. Mafita a nan kuwa, lallai ne gama garin al’umma da sauran tsirarun ‘yan siyasa masu ingiza mai kantu ruwa, a zauna a yi karatun ta-nutsu, a zamo masu hankali a jika, ba masu hankali a hannun riga ba, kuma a daina walle-walle. Idan ba haka ba to kullum za a yi ta nanata ‘yar gidan jiya ne. Wato lalume cikin duhu, da kuma dan da-na-sani. A rika lura da karin maganar malam Bahaushe inda yace, ‘’duk wanda ya shiga motar kwadayi to sai ya sauka tashar wulakanci’’. Sannan masu hakima sun ce; ‘’indai ja gaban ka hankaka ne, to kada ka yi kuka in ya bi da kai ta hanyar mushe’’. Kuma suka ce ‘’ko me ya yi ciki im bai mutu da ciki ba zai haife, in son kai ya yi ciki har ya haihu bai mutu ba, zai haifi kiyayya, in ko kiyayya ta yi ciki har ta haihu ba ta mutu ba, to za ta haifi gaba, gaba ko takan haifi bala’i. Idan lalaci ya yi ciki har ya haihu bai mutu ba, zai haifi rashi. A karshe ni ko na kara da cewa, ‘’ai jiki magayi; shan taban dan Korau’’.
sensibleyasaa@gmail.com
