SAKIYAR DA BA RUWA
by Alyasa'a Hassan on Friday, 23 March 2012 at 05:33 ·
''Najeriya
ce kasar da muke da ita, ba mu kuma da wacce ta fi ta. Wajibi ne mu
kasance a cikin ta, mu kuma hada kai wajen kyautata makomarta ta hanyar
tserar da ita daga dukkanin fitintunun da ke addabar ta''. Wadannan sune
kalmomin da manjo-Janar Muhammadu Buhari ya rufe jawabinsa na farko da
su, a ranar 31 ga watan Disamba 1983, sa'ilin da ya damki ragamar mulkin
kasar nan wanda gungun wasu Janarori suka mika masa bayan sun hambarar
da gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari. A cikin jawabin Janar
Buhari ya tabo matsalolin da suka hana kasarmu kasaita, cikinsu kuwa
harda rashin hadin kan 'yan Najeriya da rikicin kabilancin da ya biyo
bayan sakamakon zaben da aka yi watanni uku kafin a kai ga haka, da kuma
tsabar rashawa da ta haddasa tabarbarewar tattalin arzikin da ya jefa
jama'a cikin bakar wahalar da har yanzu aka kasa magancewa.
To gwamnatin Janar Buhari, da ta yi watanni goma sha tara a bisa karaga tana hobbasan ganin an kyautata al'amurar da ke wanzuwa domin talaka ya sarara, ba ta samu sukunin kawar da matsalolin da su ka sanya shi furta wadancan kalmomin ba tun farkon hawansa mulki, hasali ma kamari suka yi, suka buwaya, har sai da suka yi sanadiyyar hambarar da shi. Kasar kuma ta tsunduma cikin wani mugun yanayi mai rikitarwa da kuma tsoratarwa.
Gwamnatocin da suka biyo baya basu tabuka komai ba wajen mayar da Najeriya kasar da 'ya'yanta za su yi alfahari da ita ba, maimakon haka ma sai suka dukufa wajen saukaka dabaru da inganta hanyoyin rashawa da cin hanci, sannan kuma kwararrun ma'aikatan da aka horar da su da dukiyar talakawa ba su bi shawarar Janar Buhari ba game da bukatar da akwai wajen sadaukar da kai a gina kasa, domin sun yi ta sulalewa suna ficewa zuwa kasashen ketare inda za su samu sa'ida daga wahalhalun da suka kunno kai. Daga nan ba mai sha'awar tsayawa don tserar da ita daga fitintunun dake addabar ita. Haka nan kuma akwai gwamnatin da ta shekara takwas bayan ta Buhari babu wani abin da ta tsinana sai haddasa masifun da suka rarraba kawunan jama'ar kasa, aka daina kishin kasa, aka koma biye wa son zuciya da tsananin son kai, kowa kuma ya koma tunanin shiyyar da ya fito, da yadda za a dauki matakan hana sauran jama'ar sassan kasar cin arzikin da ba su da irin sa a yankunansu, ta yadda kowa zai jefa kifin da ya kamo cikin gorarsa.
Dalili kuwa shine wasu 'yan kudancin da ke da arzikin man fetur a shiyyarsu na yi wa 'yan wasu sashi na kasar kallon cima-zaune, wadanda basu tabuka komai wajen samar da arzikin kasa, sai dai su wanke goma su tsoma biyar idan an yi rabon arzikin kasa da su, don haka ba abin da ya fi dacewa sai kawai a kore su daga Najeriya. Wannan ne ya karfafa gwiwowin wasu matasan hafsoshin soji a karkashin Manjo Gideon Orkar har suka nemi hambarar da gwamnatin mulkin soja ta wani janar din Arewa, ranar 22 ga watan afrilun 1990, da niyyarsu na yakace shiyyar arewacin kasar nan daga tarayyar Najeriya, inda Musulmi suka yi katutu. Allah bai basu ikon haka ba, kuma har yanzu masu wannan ra'ayin ba su hakura ba, suna nan a kan bakarsu ta ganin an tsattsaga Najeriya, an ga bayan al'umman Arewar da ake kyamar addininsu, dalilin haka kuma ake ci gaba da tozarta su.
An sha daukar matakai iri-iri a lokutan mulkin Janarorin soji, musamman ma a zamanin mulkin Janar Abacha, lokacin da al'umman shiyyar Kudu-maso-Yamma suka dage wajen taka masa birki, suka rika hada baki da gwamnatocin kasashen Turai da Amurka wajen kuntata masa a kokarinsu na sai sun ga bayan sa. A lokacin ne suka dage wajen kafa kungiyar neman tsarin dimokuradiyya a kaikaice, mai suna NADECO wacce ke son a yi taron da zai samar da sukunin aiwatar da waccan muguwar manufa ta Manjo Orkar, da nufin rarraba kasar don su samu tasu Jamhuriyar da suke kira Odu'a, ko kuma Naija a yanzu don yin ban-kwana da wadanda suka kira masu mayar da hannun agogo baya, marasa sha'awar ci gaban Najeriya.
A mulkin Janar Abdussalam ma ba su hakura da wannan hankoron ta su ba. Sun kuma yi nasarar razana 'yan arewar da ke rike da mulki har sai da su ka mika musu mulkin cikin ruwan sanyi. Wannan ne matakin farko na gurgunta Arewa da jama'ar ta, kafin nan gaba a kai ga ingiza keyarsu ficewa daga tarayyar Najeriya. Bayan subucewar mulki daga hannun 'yan Arewa sai suka zame tamkar kifin da aka fitar daga ruwa, ba kuma wani abin da za su iya yi. Shi yasa jim kadan bayan Janar Olushegun Obasanjo ya hau mulki sai aka fara tunanin rarraba kan jama'ar Arewa ta hanyar addinin Musulunci domin daga bisani a ji dadin tarwatsa su. Nan take sai 'yan kudun da aka mika wa mulki suka bi, su ka kuma shishshigewa gwamnonin Arewa, suka nemi su jaddada shari'ar Musulunci a jihohinsu, amma sun yi hakan ne ba don sha'awar habakar Musulunci ba, sai dai don a ta da zaune tsaye, a tayar da fitinar da za ta farraka musulmin Najeriya. Cikin dan kankanen lokaci sai kuma makiya musulmi da Arewa suka fara zuga mabiya addinin kirista da kada su amince da shari'ar musulunci a yankunansu, har ta kai sai da aka yi ta katulan-makatulan tsakanin musulmi da kirista kan abin da kundin tsarin mulki bai haramta wa musulmi ba. Yanzu ga shi nan wancan dambarwar da aka sha yi kan Shari'a ta raunana matsayin musulmi, an kuma mance da batun aiki da ita, kuma zai yi wuya nan gaba wani ya sake bugun kirji ya ce zai karfafa shari'ar musulunci domin za a ce fitina kawai yake son tayarwa, a yi masa taron dangi a matsayin dan ta'adda.
Har yanzu dai ana nan kan wannan bakar manufar ta kuntata wa 'yan Arewa domin kuwa ana son yin taron da zai sa a mayar da musulmin kasar saniyar ware don a ji dadin korarsu daga tarayyar Najeriya, su koma can inda za su yi ta yin shari'ar musulunci don a huta da fitintunun da aka ce suna tayarwa da sunan Boko Haram.
A yanzu dai babu wanda zai iya hakikancewa ga yadda Najeriya zata kasance nan da 'yan shekaru masu zuwa, domin kuwa wani abu da zai janyo fitinar wargajewar ta na iya faruwa a ko wane lokaci. To, idan haka ya faru mutanen gabashi ba su da wata damuwa domin kuwa sun dade suna neman farfadowar kasar Biafra da suka nemi balle ta daga tarayyar Najeriya tun shekarar 1967. Su ma mutanen yamma a shirye suke su daukaka Jamhuriyar Oduduwa da suka dade suna jiran kafuwar ta idan Najeriya ta balbalce. To mu mutanaen Arewa wacce muke ciki? Sai a ranar tafiya ce za mu fafe gora, a fara hauma-hauma game da dorewar kasar da za a kafa cikin hanzari ba wani sanannen ciki? Babu wani kwakkwaran shiri dai da 'yan Arewa ke yi game da wannan batu, domin an fi mayar da hankula ne kan rikice-rikicen addini da kabilanci da ke ta rarraba kan jama'ar Arewar.
Ya dai kamata 'yan Arewa mu daga barci mu san cewa akwai wadanda ke tunanin cewa suna da wata kasa daban da Najeriya, wato masu neman kawo karshen zaman tarayya da ciyayya irin na cude-ni-in cude-ka don magance dukkan matsalolin cikinta. Bai kamata ba 'yan Arewa mu sake ayi mana sakiyar da ba ruwa idan an zo rabuwa.
Naku Alyasa'a Hassan ke muku fatan Alheri.

No comments:
Post a Comment