Saturday, 2 June 2012

Barawon Kaza Ba Zai Bar Ingarmar Doki Ba


Biki wan shagali, kowa ya raina ka ba nasa ne ba. Bikin cikar Goodluck Jonathan shekara guda bisa mulki abu ne da ya kamata a ce ya shafi daukacin ‘yan Najeriya, amma talakawa da yawa ba su ga dalilin yin murnar zagayowar ranar da aka danka masa ragamar mulki ba, domin babu wani abin kirkin da ya kulla musu. Wadanda za a ce suna murna da haka su ne jama’arsa na shiyyar kudu maso kudu, wadanda suka fi kowa amfana, sune kuma ya fifita bisa sauran, amma sai gashi nan suna nuna masa hali irin na dan masara, yana goyonsu, suna gantsara masa cizo a baya, suna kuma yi wa kasar haihuwarsu zagon kasar da ke zaizaye arzikinta.
Ashe dai murna da dangin Shugaba Jonathan suka yi, duk da sanin cewa ba abin da ya tsinana wa sauran sassan kasar, ya nuna rashin kulawarsu ga matsalolin da kasar ke ciki, wadanda kuma suka samo asali daga dabi’u da take-taken da suka biyo tsananin kawazucinsu na mulki da tsagwaron son-kai da kuma rashin kulawa da sakamakon yin hakan ya wanzar, wajen dora kasar bisa turbar karayar arziki da rashin tabbas a fannonin mulki da na siyasa.
Idan har gwamnatin Jonathan, wacce ‘yan kudu maso kudu ke garawa yadda suka ga dama, ba ta dauki matakan kawar da wadannan bala’o’in da suka riga suka kunno kai a kasar nan ba, to babu makawa hauhawar farashin kayayyaki a kasuwannin cikin gida da ya fara kamari a watannin karshe na shekarar da ta gabata, ya kuma tsananta a halin yanzu, zai ragargaza karfin Naira, har sai ganyen gyada ma ya fi ta daraja.
Karin farashin wutar lantarki da aka fara aiki da shi a wannan makon zai haddasa karancin kayayyakin da masana’antunmu na cikin gida ke samarwa, ya kuma tilasta wa bankuna kara kudin ruwa kan rancen da suke bai wa jama’a, ya kuma sa harkokin tsaro kara tabarbarewa. A yanzu kuma ragin yawan danyen man fetur da kasar Amurka ke saye daga Najeriya, a matsayinta ta babbar kasuwar danyen man kasar nan, zai jawo raguwar kudaden shiga daga danyen man-fetur,  hakan kuma na iya jawo koma-baya ga ayyukan ciyar da kasa gaba.
Ko wane daya daga cikin wadannan matsaloli da na zayyana na iya sa Najeriya ta yi mugun karko, bayan ya hankada ta cikin wahalar da za ta daidaita ta; jama’ar cikinta su farfashe. Daga nan kuma sai masifun da suka tarwatsa kasar su ja geza zuwa kasashen makwabtanmu, wadanda za su yi ta fama da tawagogin ‘yan gudun hijirar da za su fantsama can, su kuma dagula musu al’amura, su tayar da zaune tsaye. To, amma uwa-uba daga cikin wadannan matsalolin wanda ake gani zai fi saurin haddasa fitina da masifa ga arzikin kasar shi ne, satar danyen man fetur da ake ta yi gadan-gadan, domin har ma ta kai gwmnatin tarayya da kanta na fadin cewa, a cikin watanni biyar na wannan shekarar kadai, barayi sun hako danyen mai na dala biliyan bakwai.
Gwamnati ta nuna damuwarta game da wannan, amma babu wata kwakkwarar dabarar da ta kago don magance hakan, kuma an ce da sanin gwamnoni da kuma jiga-jigan ‘yan siyasan jihohin yankin ne ake yin haka. Ashe ke nan babu rana ko watan da za a daina aikata wannan ta’asar, kuma nan gaba abin na iya wuce min-sharrin ya kai ma-halaka. Da yake a yanzu asiri ya fara tonuwa game da haka, wasu gwamnonin yankin ne da kansu ke fita, don su kame jiragen ruwan da ke jigilar sataccen man: don su batar da sawun masu bincike, kada a gano masu jiragen.
Wai shin shugabannin Najeriya da kuma mu talakawa, mun taba tunanin yadda sakamakon wannan babbar ja’ibar zai iya kasancewa? Idan har tattalin arzikinmu ya ruguje gaba daya, man fetur din da ake fitarwa kasashen ketare  ya fara yin kwantai a kasuwanni, kudaden musanya ba su shigowa yadda ya kamata ai komai na iya faruwa. Wadanda za su fara cutuwa dangane da haka sune ma’aikatan gwamnatin tarayya, da na jihohi, da na kananan hukumomi, wadanda za su rasa albashinsu na wata-wata; sannan kuma miliyoyin magidanta ba za su iya ciyarwa ko tufatar da iyalansu ba; iyaye ba za su iya tura ‘ya’yansu makaranta ba; kasuwanni za su watse a ko ina a fadin tarayyar kasar nan. Fatara za ta lullube manoma; dukkan ayyukan da ake yi don farfado da tattalin arziki da inganta harkokin zamantakewa za su tsaya cik; a takaice dai tsananin damuwa da rashin kwanciyar hankali za su buwayi kasar.
Dangane da haka babu wani abin da gwamnatoci za su iya yi illa su yi ta Karin farashin man fetur da na wutar lantarki da bullo da sabbin haraji a fannonin kiwon lafiya da bayar da ilimi da kuma dukkan abubuwan da gwamnati ke yi don amfanin jama’a. Daga nan kuma harkokin kula da rayuwa za su faskara, wahalhalu za su addabi jama’a, gwamnati za ta zamo ba ta da wani tasiri ko alfanu ga rayuwar jama’a.
Yanzu dai ko na goye ya san Gwamnatin Jonathan ba za ta iya kwabar al’ummomin yankin Kudu maso Kudu (South-South), mai dimbin arzikin man fetur ba, domin kuwa sun fi karfinta, satar mai suke ta yi tukuru, ba kuma wanda ya isa ya hana su. A shekara guda da ta gabata Gwamnatin Jonathan ta sukurkuce, ta zama lusarar da ba ta iya sanyawa, ba ta kuma iya hanawa. Tana ji tana gani ake aikata ta’asa, ba ta kuma ko tsawatawa ballantana ta ladabtar da masu cabawa, don tsananin kabilanci da lalacewa. Idan ba a Najeriya ba ai babu kasar da irin wadannan kaba’iran za su ci gaba da wanzuwa ba tare da hukuma ta hukunta su ba. Shin akwai ma kasar da ta dogara kan danyen mai, amma ta mayar da filayen hakowar man tamkar gonakin gandu, sai bata-gari ne ke watayawa suna ta sassacewa?
To, ba fa dukufa wajen satar albarkatun man fetur kadai ‘yan yankin kudu maso kudu ke yi ba, sun riga sun mamaye gwamnatin Jonathan, sun kuma mai da ita tuwona-maina, su ne kadai ke cin gajiyar ta, sauran ‘yan sassan Najeriya sai dai su yi roro. Wannan ya nuna mana cewa tun suna satar dukiyar kasa ana kyalewa, wata rana daukacin danyen man za su sace karkaf, domin an ce barawon kaza ba zai bar ingarmar doki ba.

No comments:

Post a Comment

SAKIYAR DA BA RUWA

“Najeriya ce Ƙasar da muke da ita, ba mu kuma da wacce ta fi ta. Wajibi ne mu kasance a cikin ta, mu kuma haɗa kai wajen kyautata makomar...