Sunday, 22 July 2012

Jihar Filato: Abin na yi ne sai hattara!


 Wuta tun tana ‘yar karama ake kashe ta, kafin ta buwaya. Idan kuma aka bari ta gawurta, sai ta zame gagarumar gobarar da za ta janyo asara ba ‘yar kadan ba. Irin yanayin dake faruwa kenan a Jihar Filato. Wanda kuma ya samo asali ne tun a ‘yan shekarun baya, yayin da sakacin hukuma da na mahukunta suka jawo tabarbarewar al’amura har zaman lumana irin na cude-ni-in-cude-ka ya gagara. A sakamakon haka, an samu barkewar rikice-rikicen addini da na kabilanci wadanda suka fara da wasa-wasa a wasu unguwanni da kauyukan Jihar, sai gashi nan karamar magana ta zama babba. Sai da ta kai a baya aka taba yi wa musulmi kisan kiyashi a garuruwa kamar su Yelwan-Shendam da Garkawa, da ma sauran wasu kananan kauyuka dake Fadin Jihar. Rikice-rikicen a halin yanzu sunyi tsanani har ana kasa magancewa.
Abubuwan da suka haddasa wadannan masifu na da yawa. Suna kuma da sigogi barkatai masu rikitarwa. Wasu na da nasaba da kabilanci da addini, wasu kuma salsalarsu sune tsagwaron son zuciya da kulafucin abin duniya. Amma mafi girma shine sakacin mahukunta wajen dakile dalilan da suka haddasa masifun da yanzu suka zame wa al’ummomin yankin cin kwan makauniya. Ta haka ne gwamnatocin da suka gabata suka kasa shawo kansu, aka kafa dokar ta bacin da ta kawar da gwamna Joshua Chibi Dariye da majalisar dokokinsa, a wancan lokaci, na tsawon watanni shida, amma duk da haka nan ba a samu wata maslaha ba. Daga shigowar sabuwar gwamnati ma ta karkashin jogorancin Gwamna Jonah David Jang, an samu karuwar tashe-tashen hankula a fadin Jihar, an kuma sake kafa wata kwatankwacin irin wancan dokar-ta-bacin  da aka kafa wa gwamnatin da Jonah Jang ya gada, a wasu kananan hukumomin Jihar guda hudu. Su ma basu yi wani tasiri ba, hasali ma rikicin sai kara kamari suke ta yi.
Sanin kowa ne, cewa, ba wani abu ne ya jawo bala’o’in da yanzu haka ke wakana a Jihar Filato ba, illi bakar gaba, wacce hassada da ganin kyashi suka haddasa tsakanin ‘yan tsirarun kabilun Birom da suka fara zama a garin Jos, da kuma wadanda suka biyo bayansu, wato Hausa-Fulani. Wadannan kabilun su ne mafiya rinjaye daga cikin mazauna garin Jos, a wancan lokaci. Tun da farkon fari dai, ‘yan kabilar Birom su ne suka fara share wuri, suka yi zaman dirshan, kafin su haye tudun duwatsu, don tsoro da gujewa sauran kabilun da kan iya kai musu hari ko farmaki. Cikinsu kuwa har da Hausawan da idanunsu suka riga suka bude; Suka kuma dade da wayewa da sanin inda duniya ta dosa.
Allah ya albarkaci wannan wuri da kasa mai albarka da kuma dimbim ma’adinai a karkashin kasa. ‘Yan kabilar Birom dake bisa tsaunuka sun yi zamansu a haka, kuma haka nan suke noma abin da za su ci a basi tudun don tsoron mutuwa da yunwa. Su kuma Hausawa da sauran kabilu, ciki har da Angasawa masu kaunar zaman lafiya da ci gaba, sai suka yi ta gudanar da zarafinsu a karkashin duwatsun, cikin lumana da taimakon juna. Ta haka ne kowace kabila ta samu wurin zama, ta kuma ci gaba da bin tafarkin al’adu da dabi’u da ta gada kaka-da-kakanni, har kafin zuwan Turawan Ingilishi. Wadanda suka sake fasalin tsarin zamantakewar al’ummar yankin, bisa irin tsarinsu na kyama da tsana da kuma tsangwamar addinin musulunci da musulmai.
Karfafa gwiwa da Turawan suka yi wa masu sha’awar tonon kuza, suka sanya Hausawan garin Jos, bazama don neman abin duniyar da ta taimaka musu wajen gina garin Jos, har ya zamanto bashi da na biyu a zamananci a yankin arewacin Najeriya. Wannan ne ya biyo bayan fadada dogon hanyar jirgi daga Zariya zuwa Jos, don kwashe kuzar da aka hako zuwa bakin Tekun Legas, inda daga can ake yin gaba da ita zuwa nahiyar Turai. Arziki da yalwan da ya baibaye jama’ar garin Jos ne suka sa wasu daga cikin kabilun tsohon lardin Filato suka fara kyamar sauran kabilun da Allah ya kaisu can don cin arziki, har ma sai da ta kai bayan mutuwar su Sir Abubakar Tafawa Balewa, sai Janar Yakubu Gowon ya kacancala Arewa zuwa jihohi shida. Wasu na ganin cewa, an yi haka ne don kawo ci gaba, wasu kuma na cewa hakan na da nasaba ne da kokarin rugurguza arewar daidai da burin ‘yan kudun da ke kawancen siyasa da ‘yan arewa.
Dangane da haka, sai kabilun cikin jihar Binuwai-Filato suka fara tunanin janyewa daga dukkan wasu al’amura da suka hade kan jama’ar arewa. Suka kuma kakkafa nasu na kashin kansu, don hakan ya zame musu ba kare-bin-damo tsakaninsu da sauran jama’ar arewa ta yadda za su balle su samar da yankin da suka kira wai ‘Middle Belt’.
A sakamakon haka ne wasu ‘ya’yan yankin suka yunkura don hambarar da gwamnatin Janar Murtala Ramat Muhammad, domin komo da Janar Gowon, dan asalin yankin da ya hambarar bisa mulki, don cigaba da daukaka manufofi da ra’ayoyin ‘yan Middle Belt’. Bayan shekaru goma sha hudu da yin haka ba tare da nasara ba, sai kuma wasu ‘yan yankin, a karkashin Manjo Gideon Orkar suka nemi hambarar da gwamnatin Janar Badamasi Babangida don su kori  mazauna wasu bangarorin arewa daga kwaryar Jamhuriyar Najeriya. A wannan karon ma ba a ci nasara ba. To tun daga wancan lokacin, Najeriya bata zauna lafiya ba, sai masifu iri-iri masu siga da addini da kabilanci, suka rika kunno kai, ana ta tashin hankali ba kakkautawa tsakanin Hausa-Fulani da wasu kabilun jihohi daban-daban.
Wannan al’amari yafi kamari a Jihar Filato da makwabciyarta Kaduna, inda bayan anyi nasarar dandake Hausawa a siyasance, sai kuma aka koma kan danginsu Fulani wadanda hukumomin Jihar Filato suka kawar da kai sa’ilin da ake muzguna musu, ana takura musu don dai a bakanta musu ta yadda za su tsallake jihar Filaton, su bar ladansu. A nan ya zama wajibi a yi la’akari da cewa kokarin da aka sha yi a can baya don dagula al’amuran arewa, sun hada da wasu sojojin da basu san ciwon kansu ba, wadanda suka shiga cikin sabgogin hambarar da gwamnatocin mulkin soja da ‘yan arewa ke shugabanta don shimfida manufarsu ta kin jinin wasu ‘yan arewa. An gano haka a lokacin, aka kame su, aka yi musu hukuncin da yafi dacewa: hukuncin kisa.
Abin takaici game da haka shine, yadda a yanzu kuma gwamnati ke son aiwatar da abin da ya saba wa kundin tsarin mulki da karya hakkin dan Adam, wajen yunkurin tumbuke Fulanin dake zaune a wasu garuruwan da ke kananan hukumomin Barikin Ladi da Riyom, don a faranta wa abokan adawarsu rai. Wannan rashin adalci ne tsagwaronsa, domin kuwa ba Fulani ne kadai ke tayar da husuma ba, katulan-makatulan ake yi tsakaninsu da ‘yan kabilar Birom. Saboda haka nan su duka ya kamata ace sabuwar dokar tumbukewar ta shafa, domin kuwa karfe guda bashi amo.
A yanzu haka nan abubuwa marasa dadi dake wakana a jihar Filato tamkar saka ce da mugun zare ake koyawa sauran jihohin da suke ikirarin kasancewa cikin yankin Middle Belt, don su karasa aiwatar da manufar su marigayi Laftanar-kanar Bukar Dimka da Manjo Gideon Orkar don kawar da Fulani daga jihohin Kaduna, Bauchi, Gombe, Adamawa da Taraba, daga bisani kuma sai a koma kan Hausawa, da sarakunan daular Usmaniyya ta Fulani, wadanda dama tuni aka riga aka fake da batun Boko Haram aka daidaita al’ummarsu a siyasance. Yanzu dai babu sauran ta cewa, sai a yi hattara, abin na yi ne!

No comments:

Post a Comment

SAKIYAR DA BA RUWA

“Najeriya ce Ƙasar da muke da ita, ba mu kuma da wacce ta fi ta. Wajibi ne mu kasance a cikin ta, mu kuma haɗa kai wajen kyautata makomar...