Cif Edwin Kiagbodo Clark dan siyasa
ne mai fada aji a yankin Neja-Delta. Inda duk dattijo ya kai, ana iya cewa ya
kai, amma sai dai bai iya bakinsa ba. Ga shi ya manyanta matuka, ‘yan shekaru
kadan suka rage ya cika casa’in, amma dabi’u da take-takensa irin na tsohon
Najadu ne. Hasali ma a duk lokacin da Cif Edwin Clark ya buda baki, ya yi
furuci, za ka ji kamar kasa za ta tsage, za ka ji kowa na Allah-wadai da shi,
don kuwa kalamansa ko kare ma ba zai ci ba. Alheri ba ya taba fitowa daga bakinsa, sannan maganganunsa ba
yawa ba dadi.
Siyasar kabilanci ce
babbar dabi’arsa, da ita yake ci, yake sha, yake kuma takama. Wannan ne ya sa Edwin
Clark ya yi fice a karkararsu, ya kuma yi kaurin suna a kwaryar tarayyar
Najeriya. Shine ya nada kansa da kansa mukamin Jagorar kungiyar Dattijan
Neja-Delta. Kabilarsu daya da ta shugaba Jonathan, amma baya kaunarsa, domin ba
irin kutun-kutun din da bai yi wa Jonathan ba don kar ya zamo shugaban kasa.
Bayan abin ya sha karfinsa sai kuma ya komo ba shi da wani gwani kamar
Jonathan.
Ba abin da Edwin Clark ya
sanya gaba, sai sake-kake, da kulle-kullen yadda Kabilar Ijaw za ta tsere, ta
yi fin-tin-kau wa sauran kabilun yankin Neja-Delta. Ya tsani ‘yan kabilar
Itsekiri. Shi yasa ma a 2007 ya fito karara ya nuna kin amincewarsa da tsayawa
takarar Emmanuel Eduaghan a matsayin gwamnan Jihar Delta, don kabilarsu
daban-daban ne. Inda ma Cif Edwin Clark ya fi kaurin suna a ‘yan kwanakin nan,
shi ne wajen kokarin rushe tubalin ginin da ta hade kan ‘yan Najeriya, don
Kasar ta ci gaba da rushewa.
Dangane da haka, yanzu Cif
Edwin Clark shine kan gaba wajen nuna kyama da kiyayya ga yankin Arewa da
shugabanninta da kuma ‘ya’yanta. A kullum jikinsa kaikayi yake masa har idan
bai kalkalo wata jafa’in da zai malkaya wa ‘yan Arewa ba. Burinsa a ko da yaushe
shine, ya kalato kashin-kajin da zai shafa wa ‘yan Arewa don ya bakantamu a
idanun iyayen gidansa na kasashen ketare, masu kyamar jama’ar arewa da abin da
muka yi imani da shi.
A halin da ake ciki yanzu
lamarin Cif Edwin Clark ya faskara, ya fara wuce gona da iri, shi yasa ma a
‘yan kwanakin nan ya dauki karan-tsana ya dora wa gwamnonin jihohin Arewa da
tsofaffin shugabannin kasar ‘yan asalin Arewa, ba domin komai ba, sai don ya
tayar da zaune tsaye, ya ruruta wata wutar fitinar da za ta karasa daidaita
kasar.
Akan haka ne, a wajen wani
taron kungiyar lauyoyi a Abuja, ranar larabar makon jiya, Edwin Clark ya
hakikance cewa wai gwamnonin Arewa ne suka kafa kungiyar Boko-Haram domin kawai
su dagula lissafin gwamnatin Jonathan. Clark yayi amannar cewa wasu ‘yan Arewa
ne da Jonathan ya kayar a zaben 2011, masu alaka da kungiyar Boko-Haram su ke
hure kurwar gwamnatin Jonathan suke haddasa fitintinu iri-iri. Ya kuma kara da
zargin wasu da ya kira ‘yan koren da kungiyar gwamnonin Najeriya ta kafa cikin
manyan kwamitocin jam’iyyar PDP na kasa, wai su ke dafa wa gwamnonin Arewar don
kai Jonathan kasa. A cewarsa gwamnonin Arewa sun karkata akalar jam’iyyar PDP
zuwa inda suke so, sun kuma turketa a can, sai yadda suka ga dama suke yi da
ita.
To tun da yake abin na
Edwin Clark rainin wayo ne da rashin ta ido, sai gashi ya fito balo-balo yana
kalubalantar Janar Buhari, da Janar Babangida da su fito fili su wanke
kawunansu daga zargin da yake musu, na cewa suna da ruwa da tsaki game da
tashe-tashen bama-bamai da suka ki ci suka ki cinyewa a arewacin Najeriya. Ya
ce wai su fito kiri-kiri su nuna wa al’ummar kasar cewa ba su da wata alaka ko
dangantaka da kungiyar Boko-Haram. Ba irin kalaman tozartawa da Edwin Clark bai
furta ba. Ya ce wai shugabannin arewa ba wanda ya taba kai ziyara jihar Borno,
don tausayawa jama’ar da ‘yan Boko-Haram suka addaba, sai Janar Olusegun
Obasanjo ne kadai ya kai ziyara garesu don jajanta musu.
‘Yan magana suka ce
gajerar kuka dadin hawa gareta. Shin Edwin Clark ya manta cewa Shugaba Jonathan
ma bai taba zuwa ko’ina ba a Arewa don jajantawa ga jama’ar da bala’in
jefe-jefen bama-bamai suka tagayyara ba? Tsakanin shi da su Buhari wanene ya
wajaba a kansa yayi tattaki zuwa Jihar Borno don jajantawa da ba da tallafi wa
wadanda rigimar ta shafa?
Sanin kowa ne, inda Jonathan ke son kai ziyara
bayan an shirya harin ta’addanci ya kai, an kuma san wadanda ya je domin su, da
kuma dalilan da suka sa yaje din, sune kuma kadai wadanda aka taba biyan diyya
bayan an kaddamar da ta’ddancin harin bam. A game da batun manyan arewar da
yake zargin sun ki cewa uffan game da bala’o’in Boko Haram, sai a tambayi Cif
Edwin Clark, shin yana so ne su yi ikirarin su ne iyayen gidan ‘yan Boko-Haram
din? Ko so yake yi su ce da sanin su ake
tafka ta’asar da yake zargin suna haddasawa don su faranta masa rai?
To har dai idan Cif Edwin
Clark ba so yake ya bata arewa da shugabanninta ba ne, ai ya sani sarai cewa
sun sha fitowa suna kalubalantar ‘yan kungiyar Boko-Haram, da nuna musu cewa abin
da suke yi baya da nasaba da addinin musulunci. Ai ko ba komai ba za su daura yaki
su ci kasarsu ba. Yanzu wani bangaren kasar nan ne gari ya waya game da masifun
da tashin hankalin Boko-Haram ke haddasawa? Arewa da jama’ar cikinta mune kawai
muke kwaruwa musamman ma mu ‘yan arewa maso gabas (North East), sauran ‘yan
Najeriya kuwa ko a jikinsu, ba su damu da haka ba. A ganinsu tun da dai jifa ta
wuce kansu, to ta ma fada kan uban kowa mana.
Zarge-zargen da Edwin clark yake wa su Janar
Buhari ko kadan basu da makama ballantana tushe. A,a, to idan kura na da
maganin zawo me zai hana ba za tayi wa kanta ba? ‘yan arewa da wasu daga cikin
shugabanninmu mun fi kowa damuwa game da haka, sai dai babu abin da muka iya.
Wadanda daga cikinmu za su iya tabukawa don hanawa da magancewa, su kuma ba
ruwansu, matukar ba cikin gidajensu ake jefa bama-bamai ba, sun ma fi
gwammacewa al’amuran su ci gaba da tabarbarewa.
A game da gwamnonin Arewa
da Edwin Clark ya shafa wa kashin-kaji kuwa, sai ace da su Allah ya kara, ga
irinta nan ai. Ba su ne suka saki na hannu suka bi na dawa ba? Suka saki reshe
suka kama ganye? Yanzu sun gane cewa da ruwa ake shayi, domin irin sakamakon da
aka yi musu kenan, bayan da suka tayar da kura a zaben watan afrilun bara, suka
yi amfani da addini da kabilanci, suka
tayar da husumar da ta yi sanadiyyar asarar rayuka da dimbin dukiyar al’umma,
suka kuma jingina laifin tayar da tarzomar wa wasu manyan arewa.
Daga karshe kuma ga shi
nan ‘yan kudun da suka yi wa gata, sun ci, sun goge bakunansu. Tunda yake sun
ci moriyar ganga, to yanzu sakayyarsu ga ‘yan arewa ita ce ta rainin wayo da
neman ganin bayansu. A game da halin Edwin Clark kuwa, da halayen irin su
Alhaji Mujahid Asari Dokubo, da ma sauran ‘yan kudancin Najeriya, mu ‘yan arewa
ba mu da ta cewa, domin ance komai aka yi da jaki sai ya ci kara.
No comments:
Post a Comment