Saturday, 8 September 2012

A Bari Ya Huce Shi Ke Kawo Rabon Wani


 Wahalar neman albarkatun man fetur a arewacin Najeriya ya fi hakilon bidar allura a cikin rauga. Amma burin ganin an kai ga biyan bukata ba zai zama a banza ba, domin an samu burbushin man a wurare da yawa. An kuma fahimci cewa, haka za ta cimma ruwa, idan aka dukufa sosai wajen tonowa.

Dangane da haka, an ce an samu albarkatu masu tarin yawa a gabar tafkin Chadi, da ke iyaka da kasashen Kamaru da Chadi. An kuma tabbatar da cewa akwai irin wadannan albarkatun malale a gabar kogin Komadugu cikin Jihar Yobe.

To ba wadancan wurare ne kadai Allah ya tarfa wa garinsu nono ba, don a nan Jiharmu ta Bauchi ma, da makwabciyarmu Gombe, an gano cewa akwai dimbin albarkatun man-fetur a karkashin kasa, haka ma an hakikance kan cewa, akwai shi makil, a gabar kogin Binuwai.

To amma, a duk lokacin da aka ce an gano albarkatun mai a wani yanki na Arewa, sai kaga lamarin ya zame tamkar labarin kanzon kurege, musamman ma ga hukumomin gwamnatin tarayya wadanda hakkin tono man da sarrafa shi ya rataya a wuyansu.

Wani babban abin da zai kara ba ka haushi kuma, shine ganin yadda su ma a nasu bangaren, shugabannin mu na nan Arewa, babu wani hobbasa da suke yi game da haka. Hasali ma sun gwammaci su yi ta kasancewa suna dogaro da man kudun da a kullum sai an yi musu gori akai, ana musu kallon cima- zaune, wadanda sai dai su wanke goma su tsoma biyar cikin akushin arzikin kasar da ba sa tsinana komai don karuwarta.

Ko a ranar larabar da ta gabata, sai da muka ji mai girma Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, ya fito fili yana ta babatu da kame-kame kamar yadda ya saba, a wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da shi. Yana fadin cewa wai kada mutanen Arewa su rika kai kwadayinsu wajen maganar hako man Arewa. Yuguda ya ce, mutanen Arewa mu mai da hankali kan harkar noma kawai, itace kadai hanyar karuwar arziki. Domin a cewar Yuguda, wai burin Gwamnatin tarayya shine sai ta gama kwasan man da ke kudancin Najeriya, sannan za ta karaso, ta ci gaba da wawuson na Arewa. Idan ma abin da Yuguda  ya fada gaskiya ne, to ai an ce teku bata ki Karin ruwa ba. Kuma  guntun gatarin ka ya fi sari ka bani.  Dangane da wannan batu, sai a tambayi Yuguda, shin mara kishin inane shi?

Duk da cewa Gwamnatin tarayya ba ta cewa uffan game da irin dimbin arzikin man-fetur da ake samu a daya daga cikin jihohin Arewa goma sha tara, sai ga Shugaba Jonathan ya kai ziyara Jihar Anambara, inda ya tsoma ta cikin jerin Jihohin da suke da arzikin man-fetur, a matsayi ta goma. A cewar Jonathan, an gano mai a Aguleri Otu, dake yankin karamar hukumar Anambara ta gabas, har ma an kafa wata matatar mai ta musamman don sarrafa danyen man da za a rika hakowa.

To idan haka ne, me yasa bayan sanarwar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi Ibrahim Idris ya bayar na cewa an gano man-fetur a jiharsa, Gwamnatin tarayya bata sanar ba, domin a san ainahin wurin da aka gano man, da adadin yawansa, da ingancinsa?

An dai dade da fahimtar cewa akwai albarkatun man-fetur masu tarin yawa a arewacin kasarnan, amma gwamnati bata ko nuna cewa ta san da hakan. Tunda yake dai shiyyoyin Arewaci ne aka gano albarkatun mai, ai ba za a fada ba, kuma babu wani dalilin da zai sanya a tashi haikan don tonowa, tunda dai ba kaunar mu ake da arzikin ba. Amma da yake ana son yi wa Arewa rinton albarkatun man da Allah ya huwace mana, sai gashi ana cewa man da aka gano a Jihar Kogi ma wai na Jihar Anambara ne.

Wannan al’amari ne mai rikitarwa, kuma gwamnatin tarayya ta ja bakinta ta yi gum game da da’awar da Jihar Kogi ke yi, na cewa arzikin man da Jihar Anambara ke tinkaho da shi a Jihar ta Kogin aka samu. Kuma rashin daukar matakan gaggawa don bin bahasin takaddamar da za ta biyo baya game da wannan cece-kuce na iya haddasa rigima tsakanin al’ummomin jihohin biyu, masu makwabtaka da juna.

Idan kuma muka dawo kan batun rashin mayar da hankalin gwamnatin tarayya, game da kin fara hakowa da sarrafa dimbin albarkatun mai da aka gano a wurare da yawa a nan Arewa, za mu fahimci cewa, mu dinne dai al’ummar Arewa baki dayanmu ba a bukatar mu da karuwar arziki.

Suma manya-manyan kasashen yammaci da gabashin duniya, sun kwallafa ransu bisa wannan arziki da Allah ya hore mana. A sabili da haka ne ma, ake ta haddasa yamutsi da rashin kwanciyar hankali a dukkan wuraren da aka tabbatar cewa an samu man-fetur a yankin arewa. Rige-rigen da Kasashen Turai da Amurka ke ta yi don yin kaka-gida su ji dadin tatsa mana arziki, shine ya jawo fitintinun da yanzu haka suka yi kamari a jihohin Borno da Yobe. Da gangan kuma ake jingina su da addini.

To gashi nan al’amarin ya jawo mana bala’i tun kafin ma mu fara cin moriyarsa.

Idan kuma har da gaske Gwamnatin Jonathan ke yi na kara kokartawa don binciken gabar kogunan kasarnan dake kan iyakokin kasashe makwabta, musamman ma a nan arewa maso gabas, to sai ta yi himmar farawa  tun yanzu, domin ance a bari ya huce shi ke kawo rabon wani.

No comments:

Post a Comment

SAKIYAR DA BA RUWA

“Najeriya ce Ƙasar da muke da ita, ba mu kuma da wacce ta fi ta. Wajibi ne mu kasance a cikin ta, mu kuma haɗa kai wajen kyautata makomar...