Biki wan shagali, kowa ya raina
ka ba nasa ne ba. Bikin cikar Goodluck Jonathan shekara guda bisa mulki abu ne
da ya kamata a ce ya shafi daukacin ‘yan Najeriya, amma talakawa da yawa ba su
ga dalilin yin murnar zagayowar ranar da aka danka masa ragamar mulki ba, domin
babu wani abin kirkin da ya kulla musu. Wadanda za a ce suna murna da haka su
ne jama’arsa na shiyyar kudu maso kudu, wadanda suka fi kowa amfana, sune kuma
ya fifita bisa sauran, amma sai gashi nan suna nuna masa hali irin na dan
masara, yana goyonsu, suna gantsara masa cizo a baya, suna kuma yi wa kasar
haihuwarsu zagon kasar da ke zaizaye arzikinta.
Ashe dai murna da dangin
Shugaba Jonathan suka yi, duk da sanin cewa ba abin da ya tsinana wa sauran
sassan kasar, ya nuna rashin kulawarsu ga matsalolin da kasar ke ciki, wadanda
kuma suka samo asali daga dabi’u da take-taken da suka biyo tsananin
kawazucinsu na mulki da tsagwaron son-kai da kuma rashin kulawa da sakamakon
yin hakan ya wanzar, wajen dora kasar bisa turbar karayar arziki da rashin
tabbas a fannonin mulki da na siyasa.
Idan har gwamnatin
Jonathan, wacce ‘yan kudu maso kudu ke garawa yadda suka ga dama, ba ta dauki
matakan kawar da wadannan bala’o’in da suka riga suka kunno kai a kasar nan ba,
to babu makawa hauhawar farashin kayayyaki a kasuwannin cikin gida da ya fara
kamari a watannin karshe na shekarar da ta gabata, ya kuma tsananta a halin
yanzu, zai ragargaza karfin Naira, har sai ganyen gyada ma ya fi ta daraja.
Karin farashin wutar
lantarki da aka fara aiki da shi a wannan makon zai haddasa karancin kayayyakin
da masana’antunmu na cikin gida ke samarwa, ya kuma tilasta wa bankuna kara
kudin ruwa kan rancen da suke bai wa jama’a, ya kuma sa harkokin tsaro kara
tabarbarewa. A yanzu kuma ragin yawan danyen man fetur da kasar Amurka ke saye
daga Najeriya, a matsayinta ta babbar kasuwar danyen man kasar nan, zai jawo
raguwar kudaden shiga daga danyen man-fetur,
hakan kuma na iya jawo koma-baya ga ayyukan ciyar da kasa gaba.
Ko wane daya daga cikin
wadannan matsaloli da na zayyana na iya sa Najeriya ta yi mugun karko, bayan ya
hankada ta cikin wahalar da za ta daidaita ta; jama’ar cikinta su farfashe.
Daga nan kuma sai masifun da suka tarwatsa kasar su ja geza zuwa kasashen
makwabtanmu, wadanda za su yi ta fama da tawagogin ‘yan gudun hijirar da za su
fantsama can, su kuma dagula musu al’amura, su tayar da zaune tsaye. To, amma
uwa-uba daga cikin wadannan matsalolin wanda ake gani zai fi saurin haddasa
fitina da masifa ga arzikin kasar shi ne, satar danyen man fetur da ake ta yi
gadan-gadan, domin har ma ta kai gwmnatin tarayya da kanta na fadin cewa, a
cikin watanni biyar na wannan shekarar kadai, barayi sun hako danyen mai na
dala biliyan bakwai.
Gwamnati ta nuna damuwarta
game da wannan, amma babu wata kwakkwarar dabarar da ta kago don magance hakan,
kuma an ce da sanin gwamnoni da kuma jiga-jigan ‘yan siyasan jihohin yankin ne
ake yin haka. Ashe ke nan babu rana ko watan da za a daina aikata wannan
ta’asar, kuma nan gaba abin na iya wuce min-sharrin ya kai ma-halaka. Da yake a
yanzu asiri ya fara tonuwa game da haka, wasu gwamnonin yankin ne da kansu ke
fita, don su kame jiragen ruwan da ke jigilar sataccen man: don su batar da
sawun masu bincike, kada a gano masu jiragen.
Wai shin shugabannin
Najeriya da kuma mu talakawa, mun taba tunanin yadda sakamakon wannan babbar
ja’ibar zai iya kasancewa? Idan har tattalin arzikinmu ya ruguje gaba daya, man
fetur din da ake fitarwa kasashen ketare ya fara yin kwantai a kasuwanni, kudaden musanya
ba su shigowa yadda ya kamata ai komai na iya faruwa. Wadanda za su fara cutuwa
dangane da haka sune ma’aikatan gwamnatin tarayya, da na jihohi, da na kananan
hukumomi, wadanda za su rasa albashinsu na wata-wata; sannan kuma miliyoyin
magidanta ba za su iya ciyarwa ko tufatar da iyalansu ba; iyaye ba za su iya
tura ‘ya’yansu makaranta ba; kasuwanni za su watse a ko ina a fadin tarayyar
kasar nan. Fatara za ta lullube manoma; dukkan ayyukan da ake yi don farfado da
tattalin arziki da inganta harkokin zamantakewa za su tsaya cik; a takaice dai
tsananin damuwa da rashin kwanciyar hankali za su buwayi kasar.
Dangane da haka babu wani
abin da gwamnatoci za su iya yi illa su yi ta Karin farashin man fetur da na
wutar lantarki da bullo da sabbin haraji a fannonin kiwon lafiya da bayar da
ilimi da kuma dukkan abubuwan da gwamnati ke yi don amfanin jama’a. Daga nan
kuma harkokin kula da rayuwa za su faskara, wahalhalu za su addabi jama’a,
gwamnati za ta zamo ba ta da wani tasiri ko alfanu ga rayuwar jama’a.
Yanzu dai ko na goye ya
san Gwamnatin Jonathan ba za ta iya kwabar al’ummomin yankin Kudu maso Kudu
(South-South), mai dimbin arzikin man fetur ba, domin kuwa sun fi karfinta,
satar mai suke ta yi tukuru, ba kuma wanda ya isa ya hana su. A shekara guda da
ta gabata Gwamnatin Jonathan ta sukurkuce, ta zama lusarar da ba ta iya
sanyawa, ba ta kuma iya hanawa. Tana ji tana gani ake aikata ta’asa, ba ta kuma
ko tsawatawa ballantana ta ladabtar da masu cabawa, don tsananin kabilanci da
lalacewa. Idan ba a Najeriya ba ai babu kasar da irin wadannan kaba’iran za su
ci gaba da wanzuwa ba tare da hukuma ta hukunta su ba. Shin akwai ma kasar da
ta dogara kan danyen mai, amma ta mayar da filayen hakowar man tamkar gonakin
gandu, sai bata-gari ne ke watayawa suna ta sassacewa?
To, ba fa dukufa wajen
satar albarkatun man fetur kadai ‘yan yankin kudu maso kudu ke yi ba, sun riga
sun mamaye gwamnatin Jonathan, sun kuma mai da ita tuwona-maina, su ne kadai ke
cin gajiyar ta, sauran ‘yan sassan Najeriya sai dai su yi roro. Wannan ya nuna
mana cewa tun suna satar dukiyar kasa ana kyalewa, wata rana daukacin danyen
man za su sace karkaf, domin an ce barawon kaza ba zai bar ingarmar doki ba.
