
Wuta tun tana ‘yar karama ake
kashe ta, kafin ta buwaya. Idan kuma aka bari ta gawurta, sai ta zame gagarumar
gobarar da za ta janyo asara ba ‘yar kadan ba. Irin yanayin dake faruwa kenan a
Jihar Filato. Wanda kuma ya samo asali ne tun a ‘yan shekarun baya, yayin da
sakacin hukuma da na mahukunta suka jawo tabarbarewar al’amura har zaman lumana
irin na cude-ni-in-cude-ka ya gagara. A sakamakon haka, an samu barkewar
rikice-rikicen addini da na kabilanci wadanda suka fara da wasa-wasa a wasu
unguwanni da kauyukan Jihar, sai gashi nan karamar magana ta zama babba. Sai da
ta kai a baya aka taba yi wa musulmi kisan kiyashi a garuruwa kamar su
Yelwan-Shendam da Garkawa, da ma sauran wasu kananan kauyuka dake Fadin Jihar.
Rikice-rikicen a halin yanzu sunyi tsanani har ana kasa magancewa.
Abubuwan da suka haddasa
wadannan masifu na da yawa. Suna kuma da sigogi barkatai masu rikitarwa. Wasu
na da nasaba da kabilanci da addini, wasu kuma salsalarsu sune tsagwaron son
zuciya da kulafucin abin duniya. Amma mafi girma shine sakacin mahukunta wajen
dakile dalilan da suka haddasa masifun da yanzu suka zame wa al’ummomin yankin
cin kwan makauniya. Ta haka ne gwamnatocin da suka gabata suka kasa shawo
kansu, aka kafa dokar ta bacin da ta kawar da gwamna Joshua Chibi Dariye da
majalisar dokokinsa, a wancan lokaci, na tsawon watanni shida, amma duk da haka
nan ba a samu wata maslaha ba. Daga shigowar sabuwar gwamnati ma ta karkashin
jogorancin Gwamna Jonah David Jang, an samu karuwar tashe-tashen hankula a
fadin Jihar, an kuma sake kafa wata kwatankwacin irin wancan dokar-ta-bacin da aka kafa wa gwamnatin da Jonah Jang ya gada,
a wasu kananan hukumomin Jihar guda hudu. Su ma basu yi wani tasiri ba, hasali
ma rikicin sai kara kamari suke ta yi.
Sanin kowa ne, cewa, ba
wani abu ne ya jawo bala’o’in da yanzu haka ke wakana a Jihar Filato ba, illi
bakar gaba, wacce hassada da ganin kyashi suka haddasa tsakanin ‘yan tsirarun
kabilun Birom da suka fara zama a garin Jos, da kuma wadanda suka biyo bayansu,
wato Hausa-Fulani. Wadannan kabilun su ne mafiya rinjaye daga cikin mazauna
garin Jos, a wancan lokaci. Tun da farkon fari dai, ‘yan kabilar Birom su ne
suka fara share wuri, suka yi zaman dirshan, kafin su haye tudun duwatsu, don
tsoro da gujewa sauran kabilun da kan iya kai musu hari ko farmaki. Cikinsu
kuwa har da Hausawan da idanunsu suka riga suka bude; Suka kuma dade da wayewa
da sanin inda duniya ta dosa.
Allah ya albarkaci wannan
wuri da kasa mai albarka da kuma dimbim ma’adinai a karkashin kasa. ‘Yan
kabilar Birom dake bisa tsaunuka sun yi zamansu a haka, kuma haka nan suke noma
abin da za su ci a basi tudun don tsoron mutuwa da yunwa. Su kuma Hausawa da
sauran kabilu, ciki har da Angasawa masu kaunar zaman lafiya da ci gaba, sai
suka yi ta gudanar da zarafinsu a karkashin duwatsun, cikin lumana da taimakon
juna. Ta haka ne kowace kabila ta samu wurin zama, ta kuma ci gaba da bin
tafarkin al’adu da dabi’u da ta gada kaka-da-kakanni, har kafin zuwan Turawan
Ingilishi. Wadanda suka sake fasalin tsarin zamantakewar al’ummar yankin, bisa
irin tsarinsu na kyama da tsana da kuma tsangwamar addinin musulunci da
musulmai.
Karfafa gwiwa da Turawan
suka yi wa masu sha’awar tonon kuza, suka sanya Hausawan garin Jos, bazama don
neman abin duniyar da ta taimaka musu wajen gina garin Jos, har ya zamanto
bashi da na biyu a zamananci a yankin arewacin Najeriya. Wannan ne ya biyo
bayan fadada dogon hanyar jirgi daga Zariya zuwa Jos, don kwashe kuzar da aka
hako zuwa bakin Tekun Legas, inda daga can ake yin gaba da ita zuwa nahiyar Turai.
Arziki da yalwan da ya baibaye jama’ar garin Jos ne suka sa wasu daga cikin
kabilun tsohon lardin Filato suka fara kyamar sauran kabilun da Allah ya kaisu
can don cin arziki, har ma sai da ta kai bayan mutuwar su Sir Abubakar Tafawa
Balewa, sai Janar Yakubu Gowon ya kacancala Arewa zuwa jihohi shida. Wasu na
ganin cewa, an yi haka ne don kawo ci gaba, wasu kuma na cewa hakan na da
nasaba ne da kokarin rugurguza arewar daidai da burin ‘yan kudun da ke kawancen
siyasa da ‘yan arewa.
Dangane da haka, sai
kabilun cikin jihar Binuwai-Filato suka fara tunanin janyewa daga dukkan wasu
al’amura da suka hade kan jama’ar arewa. Suka kuma kakkafa nasu na kashin
kansu, don hakan ya zame musu ba kare-bin-damo tsakaninsu da sauran jama’ar
arewa ta yadda za su balle su samar da yankin da suka kira wai ‘Middle Belt’.
A sakamakon haka ne wasu
‘ya’yan yankin suka yunkura don hambarar da gwamnatin Janar Murtala Ramat
Muhammad, domin komo da Janar Gowon, dan asalin yankin da ya hambarar bisa
mulki, don cigaba da daukaka manufofi da ra’ayoyin ‘yan Middle Belt’. Bayan
shekaru goma sha hudu da yin haka ba tare da nasara ba, sai kuma wasu ‘yan
yankin, a karkashin Manjo Gideon Orkar suka nemi hambarar da gwamnatin Janar
Badamasi Babangida don su kori mazauna
wasu bangarorin arewa daga kwaryar Jamhuriyar Najeriya. A wannan karon ma ba a
ci nasara ba. To tun daga wancan lokacin, Najeriya bata zauna lafiya ba, sai
masifu iri-iri masu siga da addini da kabilanci, suka rika kunno kai, ana ta
tashin hankali ba kakkautawa tsakanin Hausa-Fulani da wasu kabilun jihohi
daban-daban.
Wannan al’amari yafi
kamari a Jihar Filato da makwabciyarta Kaduna, inda bayan anyi nasarar dandake
Hausawa a siyasance, sai kuma aka koma kan danginsu Fulani wadanda hukumomin
Jihar Filato suka kawar da kai sa’ilin da ake muzguna musu, ana takura musu don
dai a bakanta musu ta yadda za su tsallake jihar Filaton, su bar ladansu. A nan
ya zama wajibi a yi la’akari da cewa kokarin da aka sha yi a can baya don
dagula al’amuran arewa, sun hada da wasu sojojin da basu san ciwon kansu ba,
wadanda suka shiga cikin sabgogin hambarar da gwamnatocin mulkin soja da ‘yan
arewa ke shugabanta don shimfida manufarsu ta kin jinin wasu ‘yan arewa. An
gano haka a lokacin, aka kame su, aka yi musu hukuncin da yafi dacewa: hukuncin
kisa.
Abin takaici game da haka
shine, yadda a yanzu kuma gwamnati ke son aiwatar da abin da ya saba wa kundin
tsarin mulki da karya hakkin dan Adam, wajen yunkurin tumbuke Fulanin dake
zaune a wasu garuruwan da ke kananan hukumomin Barikin Ladi da Riyom, don a
faranta wa abokan adawarsu rai. Wannan rashin adalci ne tsagwaronsa, domin kuwa
ba Fulani ne kadai ke tayar da husuma ba, katulan-makatulan ake yi tsakaninsu
da ‘yan kabilar Birom. Saboda haka nan su duka ya kamata ace sabuwar dokar
tumbukewar ta shafa, domin kuwa karfe guda bashi amo.
A yanzu haka nan abubuwa
marasa dadi dake wakana a jihar Filato tamkar saka ce da mugun zare ake koyawa
sauran jihohin da suke ikirarin kasancewa cikin yankin Middle Belt, don su
karasa aiwatar da manufar su marigayi Laftanar-kanar Bukar Dimka da Manjo
Gideon Orkar don kawar da Fulani daga jihohin Kaduna, Bauchi, Gombe, Adamawa da
Taraba, daga bisani kuma sai a koma kan Hausawa, da sarakunan daular Usmaniyya
ta Fulani, wadanda dama tuni aka riga aka fake da batun Boko Haram aka daidaita
al’ummarsu a siyasance. Yanzu dai babu sauran ta cewa, sai a yi hattara, abin
na yi ne!