Tsananin son zuciya da
tsabagen rashin kishin kasa, sune illolin dake fatattaka zukatan wasu
shugabannin Najeriya, har ta kai ma a yanzu babu wani alfanun da ake samu daga ayyukan da suke zartarwa. Wannan shine
dalilin da yasa a maimakon kasar ta ci gaba, kullum sai koma baya ta ke cikin
dukkanin al’amuranta.
Tun ana kiran Najeriya ‘Giwar Africa’ tana amsawa, yanzu ce mata ake yi akuyar da ke dauke da takin da ke hana ta motsawa. Ashe dai da gaske ne da gwanayen magana ke cewa, duniya rawar ‘yan mata ce, na gaba kan koma baya. To Najeriya a yau ta zame kashin-baya, ‘yan kannenta duk sun tsere mata fintinkau, har ma tsohon shugaban kasar Ghana, Mr John Kufour, ya fahimci cewa Najeriya ta gaza, don haka a daina cewa da ita Giwar Africa.
Ko wane Shugaba da ya
shude, ya taka rawar da walau aka yaba, ko akayi Allah wadai da ita, saboda
dangartakansa da masu tatse arzikin kasarsa, Turawan da suka gaji da bautar da
kakanninmu, daga bisani suka ba mu mulkin da bai da amfani a gare mu. Tunda
bamu iya sarrafa tattalin arzikin kasarmu da kanmu, sai yadda suka ga dama za
su ta kankarar mu komai wayyo Allanmu kuma ba za su kyale mu ba.
Amma daga cikinsu babu
rawar da aka fi bata ta da tsalle kamar ta Goodluck Ebele Azikwe Mainasara
Jonathan. Saboda rashin tabukawar Jonathan wajen ciyar da kasarnan gaba, yanzu
gani ake kamar an debe wa manufofinsa ne albarka, domin tun hawansa mulki babu
wani abin alfahari guda da ya aiwatar don amfanin jama’arsa. Shugaba Jonathan
ya yi alkawurra bila-adadin, amma babu wanda ya cika.
Inda wannan al’amari ya fi
ban takaici shine, ta fuskar aikin gona. Ya sha yin alkawurran zai habaka noman
rogon da za a rika fitarwa kasashen ketare, amma duk a banza. Kai hasali ma ba
kunya ba tsoron jama’arsa, ya karya alkawarin da ya yi cewa, ya daina cin wani
burodi idan ba wanda aka yi da rogo ba.
Shugaba Jonathan ya sake
daukar wani alkawarin game da noman shinkafa. Ya ce daga shekara mai zuwa
gwamnatinsa za ta hana shigowa da shinkafa ‘yar waje, domin a koma cin shinkafa
‘yar Baro, da ake nomawa a kasarnan.
Amma me ya faru? Ai
cikin ‘yan watanni da yin wannan alkawarin sai ga gogan naka can a Kasar
Malawi inda ya kai ziyarar aiki shi da wasu gwamnoni, yana ta buga santi, yayin
da yake cin shinkafar da aka noma a can Kasar. Bayan ya cire malafar da ba
safai yake cire ta ba, a nan gida Najeriya, ya sosa sankon tsakiyar kansa, sai
ya kada baki ya ce da Shugabar Kasar Malawi Mrs Joyce Banda mai masaukinsa:
“Daga yau duk wata shinkafa da ni kaina, da jama’ata a Najeriya za su ci, daga
nan Kasar za a rika kai mana ita”.
Amma da yake babu wanda
zai iya saka masa waiji, sai kawai aka yi masa tafi: “raf-raf-raf”, gogan naka
kuwa sai kawai ya fara rausayawa, yana rangwada da wuya kamar wata sabuwar
amarya.
To a nan akwai tamabayoyi
guda biyu da suka kamata shugaba Jonathan Mai nasara ya amsa, kamar yadda
gwamna Isa Yuguda ke kiransa saboda tsabar lusaranci irin na Yuguda. Ta farko
ita ce, shin maganar noma wadatacciyar shinkafa a nan cikin gida don kawo
karshen wacce Turawa kan noma a wasu kasashe, su shigo mana da ita ta hannun
‘yan barandansu, ta sha ruwan fashi kenan? Sannan kuma zai cika wancan alkawarin da ya dauka a
gaban takwararsa Joyce Banda, game da sayen shinkafar Kasarta, ko kuma santin
banza ne ya tafka sakamakon dadin girkin da ya kwasa?
To ko ma dai menene,
talakawan Najeriya mun dade da sanin cewa, an kaimu an baro game da aikin gona,
tunda gashi ma a bana noman ya gagara saboda ka’idoji masu wahalarwa da aka
gindaya don sayar da takin zamani. Dangane da haka da wuya a samu amfanin gona
mai albarka a bana daga dan abin da ya rage bayan ambaliyan ruwan da ya halaka
gonakin manoman da dama basu samu takin ba.
Wai shin ya zama wajibi ne
sai turawa ne za su ciyar da al’ummomin kasar nan da abincin da ake nomawa a
wata duniyar can daban? A yanzu ta kai ma a duk shekara sai an kashe Naira
miliyan dubu 360, don sayo mana shinkafa daga kasashen ketare. Haka ma akan
kashe Naira milayan dubu 180 duk shekara, ko kuma a ce Naira miliyan dari biyar
a kullum don sayo alkamar da ake mana burodi ko fanken Karin kumallo. Wadannan
ba su ke nan ba, a ko wace shekara kuma sai an kashe Naira miliyan dubu 110,
don sayo sukarin da mukan sanya a kunu da koko, ko shayin da muke dunduma
kunkuru a ko wace safiya.
Idan da ace wadannan
makudan kudade aljifan manoman karkara suke shigewa, ai da tuni sun murmure,
sun tayar da komada, sun kuma san zaman rayuwa na armashi suke a Najeriya, ba
jirar mutuwa kadai ba.
An dai tabbatar da cewa,
ba iya kwanciya aka fi kare ba, sai dai a yi masa gorin mayafi. Ba finmu iya
noma, da kasa mai albarka, da matasa majiya karfi aka yi ba, sai dai a nuna
mana na’urorin zamani. To da wani dalili za a ce ba za mu iya noma abin da za
mu ci ba, har sai an kawo mana daga wata kasar dabam? Wannan ya dogara ne bisa
rashin kan-gadon shugabanninmu, wdanda Turawan Yammacin duniya ke daurewa gindi
ana zaben su ko ta halin kaka, don su ci gaba da tsiyata kasarsu na haihuwa,
kasashen Turawa kuma na ta bunkasa. Wai shin yaushe ne kan mage zai waye?