“Najeriya ce Ƙasar da muke da ita, ba mu kuma da wacce ta fi ta. Wajibi ne mu kasance a cikin ta, mu kuma haɗa kai wajen kyautata makomarta ta hanyar tserar da ita daga dukkanin fitintinun da ke addabar ta”
Waɗannan sune kalmomin da Manjo-Janar Muhammadu Buhari ya rufe jawabinsa na farko da su, a ranar 31 ga watan Disamba 1983, sa'ilin da ya damƙi ragamar mulkin Ƙasar nan wanda gungun wasu Janarori suka miƙa masa bayan sun hamɓarar da gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari.
A cikin jawabin Janar Buhari ya taɓo matsalolin da suka hana Najeriya ƙasaita, ciki kuwa harda rashin haɗin kan 'yan Najeriya da rikicin ƙabilancin da ya biyo bayan sakamakon zaɓen da aka yi watanni uku kafin a kai ga haka, da kuma tsabar rashawa da ta haddasa taɓarɓarewar tattalin arziƙin da ya jefa jama'a cikin baƙar wahalar da har yanzu aka kasa magancewa.
To gwamnatin Janar Buhari da ta yi watanni goma sha tara a bisa ƙaraga tana hoɓɓasan ganin an kyautata al'amurar da ke wanzuwa domin talaka ya sarara ba ta samu sukunin kawar da matsalolin da su ka sanya shi furta waɗancan kalmomin ba tun farkon hawansa mulki. Hasali ma ƙamari suka yi, suka buwaya, har sai da suka yi sanadiyyar hamɓarar da shi.
Tun daga wancan lokaci Najeriya ta tsunduma cikin wani mugun yanayi mai rikitarwa gami da tsoratarwa.
Gwamnatocin da suka biyo baya basu taɓuka wani abin a-zo-a-gani ba don mayar da Najeriya irin Ƙasar da 'ya'yanta za su yi alfahari da ita ba. Maimakon haka ma sai suka duƙufa wajen sauƙaƙa dabaru da inganta hanyoyin rashawa da cin hanci. Su ma ƙwararrun ma'aikatan da aka horar da su da dukiyar talakawa ba su bi shawarar Janar Buhari ba game da buƙatar da ke akwai wajen sadaukar da kai a gina Ƙasa. Sun yi ta sulalewa suna ficewa zuwa ƙasashen ƙetare inda za su samu sa'ida daga wahalhalun da suka kunno kai.
Daga nan ba mai sha'awar tsayawa don tserar da Najeriya daga fitintunun dake addabar ta.
Haka nan kuma akwai gwamnatin da ta shekara takwas bayan ta Buhari babu wani abin da ta tsinana sai haddasa masifun da suka rarraba kawunan jama'ar ƙasa, aka daina kishin ƙasa, aka koma biye wa son zuciya da tsananin son kai, kowa kuma ya koma tunanin shiyyar da ya fito, da yadda za a ɗauki matakan hana sauran jama'ar sassan ƙasar cin arziƙin da ba su da irin sa a yankuna su ta yadda kowa zai jefa kifin da ya kamo cikin gorarsa.
Dalili kuwa shine tun a wancan lokaci wasu 'yan kudancin da ke da arziƙin man fetur a shiyyarsu na yi wa 'yan Arewa kallon cima-zaune, waɗanda basu taɓuka komai wajen samar da arziƙin ƙasa, sai dai su wanke goma su tsoma biyar idan an yi rabon arziƙin ƙasa da su, don haka ba abin da ya fi dacewa sai kawai a raba Ƙasar kowa ya kama gabansa.
An sha ɗaukar matakai iri-iri a lokutan mulkin Janarorin soji, musamman ma a zamanin mulkin Janar Abacha, lokacin da al'umman shiyyar Kudu-maso-Yamma suka dage wajen taka masa birki, suka riƙa haɗa baki da gwamnatocin ƙasashen Turai da Amurka wajen ƙuntata masa a ƙoƙarinsu na sai sun ga bayan sa. A lokacin ne suka dage wajen kafa kungiyar neman tsarin dimokuraɗiyya a kaikaice, mai suna NADECO wacce ke son a yi taron da zai samar da sukunin aiwatar da waccan muguwar manufa ta su, da nufin rarraba ƙasar don Yarbawa su samu tasu Jamhuriyar da suke kira Odua ko kuma Naija, su ma Inyamurai su samu tasu Biafara da suka jima suna hanƙoron kafa ta, don yin ban-kwana da waɗanda suka kira masu mayar da hannun agogo baya, marasa sha'awar ci gaban Najeriya.
A mulkin Janar Abdussalam ma ba su haƙura da wannan hanƙoron ta su ba. Sun kuma yi nasarar razana 'yan Arewar da ke riƙe da mulki har sai da su ka miƙa musu mulkin cikin ruwan sanyi, wautar da ya kasance matakin farko na gurgunta Arewa da jama'ar ta, kafin nan gaba a kai ga ingiza ƙeyarsu ficewa daga tarayyar Najeriya.
Bayan suɓucewar mulki daga hannun 'yan Arewa sai waɗanda a ke gani sune manyan ta suka zame tamkar kifin da aka fitar daga ruwa, ba kuma wani abin da za su iya yi don cigaban al'ummar ta.
Wannan ne dalilin da yasa jim kaɗan bayan Janar Olushegun Obasanjo ya hau mulki sai aka fara tunanin rarraba kan jama'ar Arewa ta hanyar addinin Musulunci domin daga bisani a ji daɗin tarwatsa su.
Nan take sai 'yan kudun da aka miƙa wa mulki duk suka bi suka shishshigewa gwamnonin Arewa, suka nemi su jaddada shari'ar Musulunci a jihohinsu, ba don sha'awar haɓakar Musulunci ba, sai dai don a ta da zaune tsaye, a tayar da fitinar da za ta farraka musulmin Najeriya.
Cikin ɗan ƙanƙanen lokaci sai kuma maƙiya musulmi da Arewa suka fara zuga mabiya addinin kirista 'yan asalin Arewa, da kada su amince da shari'ar musulunci a yankunansu, har ta kai sai da aka yi ta katulan-makatulan tsakanin musulmi da kirista kan abin da kundin tsarin mulki bai haramta wa musulmi ba.
Yanzu ga shi nan wancan dambarwar da aka sha yi kan Shari'a ta raunana matsayin musulmi, an kuma mance da batun aiki da ita, kuma zai yi wuya nan gaba wani ya sake bugun ƙirji ya ce zai ƙarfafa shari'ar musulunci domin za a ce fitina kawai yake son tayarwa, a yi masa taron dangi a matsayin ɗan ta'adda.
Har yanzu dai ana nan kan wannan baƙar manufar ta ƙuntata wa 'yan Arewa domin kuwa ana son yin taron sake fasalta jadawalin Ƙasar da zai sa a mayar da musulmin kasar saniyar ware don a ji dadin korarsu daga tarayyar Najeriya, su koma can inda za su yi ta yin shari'ar musulunci don a huta da fitintunun da aka ce suna tayarwa da sunan Fulani makiyaya da Boko Haram.
A yanzu dai babu wanda zai iya haƙiƙancewa ga yadda Najeriya zata kasance nan da 'yan shekaru masu zuwa, domin kuwa wani abu da zai janyo fitinar wargajewar ta na iya faruwa a ko wane lokaci.
To, idan haka ya faru mutanen gabashi ba su da wata damuwa domin kuwa sun daɗe suna neman farfaɗowar kasar Biafra da suka nemi ɓalle ta daga tarayyar Najeriya tun shekarar 1967. Su ma mutanen yamma a shirye suke su ɗaukaka Jamhuriyar Oduduwa da suka daɗe suna jiran kafuwar ta idan Najeriya ta ɓalɓalce.
Arewa fa! wacce muke ciki? Sai a ranar tafiya ce za mu fafe gora, a fara hauma-hauma game da ɗorewar wata sabuwar ƙasar da za a kafa cikin hanzari ba wani sanannen shiri?
Babu wani ƙwaƙƙwaran shiri dai da 'yan Arewa ke yi game da wannan batu, domin an fi mayar da hankula ne kan rikice-rikicen addini da kabilanci da ke ta rarraba kan jama'ar Arewar.
Ya dai kamata 'yan Arewa mu farka daga barci mu san cewa akwai waɗanda ke tunanin cewa suna da wata ƙasa daban da Najeriya, wato masu neman kawo ƙarshen zaman tarayya da ciyayya irin na cude-ni-in cude-ka don magance dukkan matsalolin cikinta. Bai kamata ba 'yan Arewa mu sake ayi mana sakiyar da ba ruwa idan an zo rabuwa.
Alyasa'a Hassan 03–06–2017